Gen. Tchiani |
Jagoran juyin mulkin da aka yi Nijar ya yi Allah-wadai da takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta sanyawa ƙasar, yana mai bayyana su a matsayin abin da ya saɓawa doka da kuma rashin adalci.
Cikin wani sako da ya gabatarwa al'ummar ƙasar ta talbijin, janar Abdoramane Tchiani, ya ce gwamnatinsa ba zata yarda ƙasashen yamma ko na yankin Afirka su matsawa ƙasarsa lamba a kan a mayar da Bazoum kan shugabanci ba.
Janar Tchiani ya kuma ce kada ƴan ƙasar Faransa su ji fargabar komai.
Tuni dai Faransa ta kwashe mutane kusan dubu guda ciki har da ƴan ƙasarta 560, bayan da masu bore suka kai wa ofishin jakadancinta a Yamai hari a ranar Lahad
1 Comments