Kudirin tashar Arewa 24 da ya sanya was wasi ga mabiyan ta

Hoton mai gabatar da shirin Mata A Yau na Arewa24 
Cecekucen ya kunno kai ne a shafukan sada zumunta musamman a dandalin twitter da aka musanyawa suna izuwa X. Ma su amfani da shafin da dama na ta wallafa rubutun kin jinin shirin "Mata a Yau" bisa zargin fadin wasu kalaman da zasu tunzura matan Aure.

Mata a Yau, shirin talabijin ne na tashar Network AREWA24 Limited wanda akafi sani da Arewa24 da ke yadda shirye shiryen ta kan tauraron dan adam ta DSTV, GOtv, da Startimes da ke baje kolin salon rayuwar yankin Arewacin Najeriya. Kuma shirin yana maida hankali ne kan rayuwan ya'ya mata.
Toh sai dai wasu mabiya wannan tasha sun fara korafi, inda suke zargin shirin Mata A Yau na tashar da tabargaza maimakon gyara. 

Kazalika mabiya tashar na korafi kan yadda masu gabatar da shirin wato A'isha Umar Jajere, Halima Ben Umar da kuma Hafsat A.B Hamza na furta wasu kalamai da ma bada misalan da ka iya tunzura dabi'un matan aure har ma yayi sanadiyar mutuwar auren su.
Ga ma wasu daga cikin rubuce rubucen da wasu masu amfani da shafin Twitter wato X sukayi na sukar shirin Mata a Yau.
Yayin da wasu ke ganin cewa tashar Arewa 24 ta shirya wannan shirin ne domin gurbata tunanin matan aure, wasu kuma gani suke shirin na da kyakkyawar manufa ga Makomar zaman aure musamman a arewacin najeriya.
Duk da bambancin ra'ayi da makalata wannan tasha ke dashi dangane da shirin Mata A Yau, ya kyautu hukumar lura da kafafen watsa labarai tayi duba kan wannan lamari domin tsabtace shi.

Comments

Read Also